Asabar 24 Oktoba 2026 - 21:46
Karatun Muhawara | Amsoshi Masu Ban Mamaki na Imam Ridha (A.S.) ga Tambayoyin Mai Musun Samuwar Allah

Hauza/ Wata tattaunawa mai jan hankali tsakanin Imam Ridha (A.S.) da wani mutum mai musun samuwar Allah, inda Imam (A.S.) ya yi amfani da hujjoji bayyanannu kuma masu sauƙin fahimta, yana bayyana cewa gazawar gaɓoɓin ji wajen fahimtar Allah ba hujja ba ce ta musun samuwarsa. Haka kuma, ya yi amfani da alamomin halitta wajen tabbatar da samuwar Allah.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, littafin *Muhawara 101 Masu Ban Sha’awa da Jan Hankali*, wanda Muhammad Muhammadi Ishtihardi ya rubuta, ya tattara muhawarori daban-daban kan batutuwan akida da addini. Shafin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza  zai riƙa wallafa waɗannan muhawarori a sassa daban-daban.

Muhawarar Imam Ridha (A.S.) da Wani Mai Musun Samuwar Allah

Wani mutum da yake musun samuwar Allah ya zo wajen Imam Ridha (A.S.). A lokacin, akwai wasu mutane da suke zaune a wurin Imam. Sai Imam (A.S.) ya ce masa: “Idan gaskiya tana tare da ku — alhali kuwa ba haka ba ne — to, a wannan yanayin, mu da ku za mu zama daidai. Sannan sallah, azumi, zakka da imaninmu ba za su cutar da mu da komai ba. Amma idan gaskiya tana tare da mu — kamar yadda yake a zahiri — to, mu za mu rabauta, ku kuma za ku yi asara, ku faɗa cikin halaka.”

Mai musun samuwar Allah: Ka gaya mini, yaya Allah yake, kuma ina yake?

Imam Ridha (A.S.): “Kaiconka! Hanyar da kake bi ba daidai ba ce. Allah Maɗaukaki ne ya halicci ‘yadda abu yake’, ba tare da shi kansa an siffanta shi da wata irin ‘yadda’ ba. Haka kuma, ya halicci wuri, ba tare da shi kansa yake da wani wuri ba.

Saboda haka, ba a sanin zatinsa tsarkakakke ta hanyar tambayar yadda yake ko inda yake. Haka kuma, babu wata gaɓar ji da za ta iya fahimtar zatinsa, kuma ba ya kama da komai.”

Mai musun samuwar Allah: Idan babu wata gaɓar ji da za ta iya fahimtar Allah, to, wannan yana nufin cewa shi ba wani abu ba ne.

Imam Ridha (A.S.): “Kaiconka! Saboda gaɓoɓin jikinka sun kasa fahimtar Allah ne za ka musanta samuwarsa? Alhali kuwa mu, duk da cewa gaɓoɓin jikinmu ma ba za su iya fahimtar zatinsa tsarkakakke ba, muna yin imani da shi, kuma muna da yaƙinin cewa shi ne Ubangijinmu, wanda bai kama da komai ba.”

Mai musun samuwar Allah: Ka gaya mini, tun yaushe Allah yake?

Imam Ridha (A.S.): “Ka gaya mini, yaushe ne Allah bai kasance ba, domin in gaya maka tun yaushe ya kasance.”

Mai musun samuwar Allah: Wace hujja ce take tabbatar da samuwar Allah?

Imam Ridha (A.S.): “Idan na kalli jikina, sai na ga cewa ba zan iya ƙara ko rage wani abu a tsawonsa ko faɗinsa ba. Haka kuma, ba zan iya kawar da lahani da munanan abubuwa daga gare shi ba, ko kuma in samar masa da abin da zai amfane shi.

Daga nan ne na samu yaƙinin cewa wannan ginin na jiki yana da wanda ya gina shi, kuma na yarda da samuwar Mahalicci.

Baya ga haka, zagayawar taurari da sauran duniyoyi, samuwar gizagizai, busawar iska, da motsin rana, wata da taurari, duk waɗannan alamu ne da suke nuna cewa waɗannan abubuwa masu zagayawa suna da wanda yake tafiyar da su, kuma waɗannan halittu suna da Mahalicci da Mai gudanar da al’amuransu.”¹

Manazarta 

¹. Usulul-Kafi, juzu’i na 1, shafi na 78.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha